Isa ga babban shafi

"Tilas a kawo karshen bai wa kungiyoyin 'yan ta'adda kudaden fansa"

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari, ya bukaci kawo karshen biyan kudaden fansa ga kungiyoyin ‘yan ta’adda a nahiyar Afrika.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, yayin jawabi ga kwamitin tsaron kungiyar tarayyar Afrika AU, a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.a
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, yayin jawabi ga kwamitin tsaron kungiyar tarayyar Afrika AU, a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.a TheCable
Talla

Buhari ya yi kiran ne, yayin gabatar da jawabinsa a taron kwamitin tsaron kungiyar taryyar Afrika AU, wanda ke gudana birnin Addis Ababa da ke karbar bakuncin taron kungiyar AU, karo na 30.

Shugaban Najeriyar, ya ce toshe kafar da kungiyoyin ‘yan ta’adda ke samun kudade yana da matukar muhimmanci wajen murkushe su, kasancewar karfin soja kadai ba zai iya samar da cikakkiyar nasara ba.

Buhari ya yabawa kasashen da ke kawance da Najeriya wajen yakar ta’addancin kungiyar Boko Haram a yankin tafkin Chadi, inda ya bukaci kara azama kasancewar har yanzu akwai ragowar barazanar mayakan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.