Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

ANC ta kammala shirin soke Zuma daga Mulki

Jam’iyyar ANC da ke Mulki a Afrika ta Kudu ta tabbatar da cewa tana gab da kawo karshan shugabancin Jacob Zuma da ake zargi da badakalar rashawa a tsawon mulkinsa na shekaru 9.

Shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma na cikin tsaka-mai-wuya
Shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma na cikin tsaka-mai-wuya REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Zuma dai na ci gaba da fuskantar matsin lamba tun lokacin da ‘yan siyasa dama kungiyoyin farraren hulan kasar suka bukaci ya yi murabus.

A kwanan baya magoya bayan jam’iyyar ANC suka zabi mataimakin Shugaba kasar Cyril Ramaphosa dan maye gurbinsa a matsayin shugaban jam’iyya.

Magoya bayan Ramaphosa dai na kan gwiwar gani lallai Zuma ya sauka domin mataimakin da ake gani zai farfado da tatalin arzikin kasar ya gaji kujerar.

Wasu rahotanni kafafa yadda labaran kasar na ce kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na shirye-shiryen mikawa Jacob Zuma bukatar sauka daga mulki idan kuma ya ki, shugancin jam’iyyar zai tsige shi da karfin tsiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.