Isa ga babban shafi
africa ta kudu

'Yan Najeriya na fuskantar hare-hare a Africa ta kudu

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari anguwar ‘yan Najeriya mazauna Afrika ta kudu tare da kone musu gidaje da shagunan kasuwanci a yankin Krugersdorp da ke gab da birnin Johannesburg.

'Yan bindigar wadanda 'yan asalin Africa ta kudu ne, na ci gaba da kone gidaje makarantu dama shagunan kasuwanci mallakin 'yan Najeriya da ke kasar.
'Yan bindigar wadanda 'yan asalin Africa ta kudu ne, na ci gaba da kone gidaje makarantu dama shagunan kasuwanci mallakin 'yan Najeriya da ke kasar. Reuters
Talla

Kamfanin dillacin labaran Najeriya NAN, ya ruwaito shugaban al’ummar Najeriya mazauna yankin Mr Cyril James ta wayar tarho na cewa ‘yan bindigar ‘yan asalin kasar ne kuma sun fara kai hare-haren ne tun daga ranar 18 ga watan nan.

Mr James, ya ce mutanen sun yi zargin wani dan Najeriya da sace wata budurwa ‘yar Afrika ta kudun tare da yi mata fyade, lamarin da ya sanya daukar fansa kan duk wani dan Najeriya da ke kasar, duk da cewa an gano babu gaskiya a zargin.

A cewar James kawo mutum biyu sun mutu haka zalika akwai daruruwan wadanda suka samu muggan raunuka sanadiyyar harin, dalilin da ya tilastasu barin unguwar don tsira da rayukansu ba kuma tare da daukan dukiyar da suka mallaka ba.

Shugaban ya kuma bukaci hukumomin Najeriya su dauki matakan gaggawa tun kafin abin ya kara tsananta, la’akari da cewa ‘yan bindigar na wani sabon shirin kai musu hari.

A nasa bangaren shugaban al’ummar Najeriya a kasar ta Afrika ta kudu Mr Adetola Olubajo, ya ce al’amarin ya tsananta, kuma babu tabbacin tsaron rayukan ‘yan Najeriyar da ke yankin ganin cewa babu mai taimaka musu.

Mr Olujoba anda ya bayyana harin dana kin jinin baki ko a makwanni biyu da suka gabata sai da wani dan Tasi ya kone akalla shaguna biyar na ‘yan Najeriya, babu kuma matakin da aka dauka.

A cewar kungiyar ta ‘yan Najeriya mazauna Afrika ta kudu, tun da farko sai da suka mika mutumin da ake zargi da yiwa yarinyar fyade amma bayan gudanar da shari’a aka gano cewa zancen kanzon kurege ne.

Ko a bara ma dai al’ummar Afrika ta kudu sun yi ta kai munanan hare-hare kan ‘yan Najeriya mazauna kasar tare da hallaka mutane da dama ba kuma tare da daukar kwararan matakai ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.