Isa ga babban shafi
TANZANIA

Magafuli ya haramta rijistar jiragen ruwan kasashen ketare

Shugaban Tanzania John Magafuli ya sanya wata sabuwar dokar wucin gadi da za ta haramta yiwa jiragen ruwa na kasashen ketare rijista tare da umartar gudanar da bincike kan wasu jirage fiye da 400 don gano ko suna da hannu a ayyukan ta’addanci.

Galibin jiragen ruwan kasashen da ke da takunkumi aka ko kuma wadanda ke son safarar miyagun kayaki kan yi amfani da tutar kasar Tanzaniyar don ketare tekuna ba tare da tuhuma ba.
Galibin jiragen ruwan kasashen da ke da takunkumi aka ko kuma wadanda ke son safarar miyagun kayaki kan yi amfani da tutar kasar Tanzaniyar don ketare tekuna ba tare da tuhuma ba. eu.greekreporter.com
Talla

Matakin na Magafuli na zuwa ne bayan da aka kame akalla jiragen ruwa 5 a sassan duniya makare makamai wasu lokutan kuma da haramtattun kayaki amma kuma dauke da tutar kasar.

Ko a shekarun baya ma hukumomin da ke kula da gabar tekun Indiya sun sha kame jiragen ruwan kasashen Iran da Korea ta arewa na safarra kayaki duk da takunkuman da majalisar dinkin duniya da ke kansu sakamakon amfani da tutar Tanzania

Wata sanarwa da fadar shugaba John Magafuli ta fitar ta ce za a dakatar da aikin rijistar jiragen ruwan har zuwa wani lokaci da nufin tantancewa baya ga tsanannta bincike don gano jiragen da ke munanan harkalla.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.