Isa ga babban shafi

Najeriya ta nemi hadin-kan ECOWAS don dakile yaduwar makamai a kasashensu

Gwamnatin Najeriya ta nemi hadin-kan kungiyar ECOWAS wajen kawo karshen yaduwar kananan makamai da ke barazanar ga zaman lafiyan kasashen.

Shugaba Muhammadu Buhari ya lashi takobi hukunta masu haifar da rikice-rikice a Najeriya
Shugaba Muhammadu Buhari ya lashi takobi hukunta masu haifar da rikice-rikice a Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Ministan harkokin cikin gidan Kasar Abdurrahman Bello Dambazau, da ya kai ziyara hedikwatar kungiyar da ke Abuja, ya ce akwai tabbacin cewar yaduwar kananan makamai na cikin abubuwan da ke kara hura wutar rikicin makiyaya da manoma.

Janar Dambazau mai ritaya na gani tabbatar da zaman lafiya a kasashen ECOWAS ba zai samu ba muddin aka zura ido kananan makamai na ci gaba da yawo tsakanin kasashen yankin.

Ministan ya ce rashin bin dokar da aka shata na ratsa iyakokin kasa da kasa shi ma ya taka rawa wajen haifar da munanan rikicin makiyaya da manoma da ake samu a kasashen na ECOWAS.

Kwamishinan da ke kula da harkan kasuwanci da yawo cikin walwala na ECOWAS, Alhaji lawali shuaibu, ya ce sun gamsu da hujojjin Najeriya kuma nan gaba kadan za su shirya taro da zai mayar da hankali kan wadanan matsaloli domin duba matakan da ya kamata a dauka.

Rikicin Makiyaya da Manoma da ke sanadin rayuka ba a Najeriya ka dai ake fama dashi ba, hadda sauran kasashen ECOWAS dama Afirka baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.