Isa ga babban shafi
Liberia

Jam'iyya mai mulki a Liberia ta kori shugaba Sirleaf

Jam’iyyar UP mai mulki a Liberia ta kori shugabar kasar, Ellen Johnson Sirleaf mai barin gado sakamakon zargin ta da yin katsalandar a zaben shugabancin kasar da nufin mara wa Gorge Weah na jam’iyyar adawa da ya doke mataimakinta, Joseph Boakai.

Shugabar Liberia mai barin gado Ellen Johnson Sirleaf
Shugabar Liberia mai barin gado Ellen Johnson Sirleaf REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Uwargida Sirleaf da ta shafe tsawon shekaru 12 akan karagar mulki, ta musanta zargin da jam’iyyarta ke yi ma ta na ganawa akai akai da hukumomin zabe gabanin ranar 10 ga watan Oktoban bara, wato ranar da aka kada kuiri’u a zagayen farko na zaben kasar.

Baya ga Sirleaf, har ila yau jam’iyyar ta UP ta sallami wasu manyan mambobinta hudu kamar yadda ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Lahadi.

Sanarwar ta ce, an dauki matakin koran mutanen ne saboda yi wa jam’iyyar zagon kasa da kuma kaskantar da kimarta.

An dai tuntubi ofishin shugaba Sirleaf don yin tsokaci kan wannan mataki amma kawo yanzu bai ce uffan ba.

Tsohon dan kwallon kafar duniya, Goerge Weah ne dai ya lashe zaben mai cike da tarihi bayan ya doke mataimakin shugaban kasa Joseph Boakai da gagarumin rinjaye, lamarin da a karon farko cikin shekaru 70 zai kai ga mika mulki daga gwamnatin demokradiya zuwa wata gwamnatin ta demokradiya.

Baraka ta fito fili ne tsakanin shugaba Sirleaf da mataimakinta Boakai a lokacin yakin neman zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.