Isa ga babban shafi

Jakadun Nahiyar Afrika sun bukaci Trump ya nemi afuwarsu

Ilahirin Jakadun kasashen nahiyar Afrika a zauren Majalisar Dinkin Duniya, sun bukaci shugaban Amurka Donald Trump da ya nemi afuwa dangane da kalaman cin zarafi da ya furta kan al’ummar nahiyar da kuma kan wasu kasashe na yankin Carribean.

Martha Ama Akyaa Pobee Jakadiyar kasar Ghana a Zauren Majalisar Dinkin Duniya.
Martha Ama Akyaa Pobee Jakadiyar kasar Ghana a Zauren Majalisar Dinkin Duniya. YouTube
Talla

Trump ya furta kalaman cin zarafin ne yayin da yake ganawa da ‘yan majalisar dattawan kasar a fadar White House ranar Alhamis.

Trump ya soki yadda baki ‘yan ci rani ke kwarara zuwa Amurka daga nahiyar Afrika, da kuma kasashen El Salvador da Haiti, wadanda ya bayyana a matsayin matalauta, kuma kazamai.

Bayan kammala taron da suka yi, mai magana da yawun Jakadun kasashen nahiyar Afrika a zauren Majalisar Dinkin Duniya Martha Ama Akyaa Pobee da ke wakiltar kasar Ghana, ta yi alla wadai da kalaman na Trump, wadanda ta suka bayyana a matsayin na nuna wariyar launi da ketare iyaka, dan haka jakadun suka bukaci shugaban ya janye kalaman, tare da fitowa fili ya nemi afuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.