Isa ga babban shafi
Afrika ta kudu

Sabon jagoran ACN ya kalubalanci Jacob Zuma

Sabon jagoran jam’iyyar ANC a Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa ya kalubalanci shugabancin kasar a matsayin wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen kassara tattalin arziki tare da haddasawa jam’iyyar bakin jini a idon al’umma.

Jagoran na ANC Cyril Ramaphosa da ya jagoranci gangamin cikar jam'iyyar shekaru 106 da kafuwa ya zargi tsohon shugaban da lalata ta.
Jagoran na ANC Cyril Ramaphosa da ya jagoranci gangamin cikar jam'iyyar shekaru 106 da kafuwa ya zargi tsohon shugaban da lalata ta. REUTERS/Rogan Ward
Talla

Duk da cewa Ramaphosa bai fito karara ya bayyana sunan Jacob Zuma a matsayin wanda ya tagayyara jam’iyyar ba, amma ya ce matukar ana bukatar dawo da martabar ta to dole ne sai an kawar da wadanda suka kassara ta.

Ramaphosa wanda ke jawabi yayin gangamin cikar jam’iyyar ta ANC shekaru 106 da kafuwa, ya ce matukar mambobin jam’iyyar na bukatar nasara a zabe mai zuwa to dole ne fa sai jam’iyyar ta zamo tsintisya guda tare da dawo da martabar da ta rasa a idon duniya.

A baya shugaba Jacob Zuma ya yi ta fuskantar zarge-zargen cin hanci lamarin da ya kai ga kada kuri’ar yankan kauna don kawo karshen mulkinsa, amma a lokuta da dama yana musanta hakan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.