Isa ga babban shafi
Morocco

Morocco ta kammala kwashe al'ummarta da ke Libya

Morocco ta sanar da kammala jigila ta uku kuma ta karshe don kwashe al’ummarta da ke zaune a Libya, a kokarinsu na tsallakawa Nahiyar Turai don ci rani.Kasar ta bi sahun kasashen Nahiyar Afrika da suka gudanar da aikin kwashe al'ummarsu daga Libyan, tun bayan gano yadda ake cinikin bayi a kasar.

Wasu tarin 'Yan cirani kenan a kokarinsu na tsallakawa Nahiyar Turai daga Libya.
Wasu tarin 'Yan cirani kenan a kokarinsu na tsallakawa Nahiyar Turai daga Libya. REUTERS/Hani Amara
Talla

Ma’aikatar da ke kula da ‘yan ci rani a Morocco ta ce cikin jigilar da aka fara Juma’ar da ta gabata an dawo da kimanin ‘yan kasar 338 gida ta hanyar amfani da jirgin Afriqiyya na Libya, daga bisani kuma bayan dawowarsu Morocco aka sanya su a manyan motoci don mayar da su yankunan da suka fito.

Ma'aikatar ta ce ta sada dukkanin 'yan ci ranin da iyalansu tare da daukar matakan ganin ba'a ci gaba da samun 'yan kasar da ke ficewa don ci rani a Turai ba.

A baya ma Morocco ta kwashe akalla ‘yanci rani 435 cikin jigila biyu da ta yi a watan Agusta da Disamban bara tun bayan bankado asirin ciniki da kuma bautar da bakaken fata dama sauran 'yan ci rani a Libyan.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta bukaci Libyan ta kulle wasu cibiyoyi akalla 30 da ake rike da ‘yan ci rani fiye da dubu 15.

Libya ita ce hanya mafi sauki da bakin hauren kan yi amfani da ita don tsallakawa Nahiyar Turai, inda kuma da dama kan gamu da ajalinsu yayin tsallakawa Tekun Mediterraniean.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.