Isa ga babban shafi

Kungiyar ISGS ta yi Ikirarin kai wa sojin Amurka da Faransa hare-hare

Wata kungiya mai da’awar Jihadi da ke kiran kanta da sunan ISGS a takaice, wadda kuma ke alakanta kanta da kungiyar IS, ta dauki alhakin kai wa sojojin Amurka da na Faransa hare-hare a sassan yammacin nahiyar Afrika.

Wasu sojojin kasar Mali, yayin da suke sintiri a birnin Bamako, Mali. 22, Nuwamba, 2015.
Wasu sojojin kasar Mali, yayin da suke sintiri a birnin Bamako, Mali. 22, Nuwamba, 2015. Issouf Sanogo/AFP
Talla

Cikin sanarwar da kamfanin dillancin labarai na kasar Muritania ya wallafa, kungiyar karkashin shugabancin Adnan Walid Sahraoui, ta yi ikirarin cewa, ita ce ta hallaka sojin Amurka 4, a harin da ta kai musu cikin watan Oktoba na shekarar 2017 a Jamhuriyar Nijar, a kauyen Tongo Tongo da ke kan iyakar kasar da Mali.

Zalika kungiyar ta dauki alhakin kai harin kunar bakin wake na ranar Alhamis din da ta gabata, a yankin arewa maso gabashin kasar Mali, wanda ya yi sanadin raunata sojojin Faransa 3.

Harin na ranar Alhamis ya zo dai dai da cika shekaru 5, da fara kokarin murkushe ayyukan ta’addanci a arewacin Mali a karkashin jagorancin sojin Faransa.

A farkon shekara ta 2012 ne, kungiyar mayakan ta ISGS, da a waccan lokacin ta ke alakanta kanta da kungiyar al-Qaeda, ta kwace iko da yankin arewacin kasar Mali, amma daga bisani sojojin Faransa suka jagoranci yakarsu, lamarin da ya tilasta musu tserewa daga yankunan suka mamaye.

Har yanzu dai mayakan suna ci gaba da kai wa sojojin Faransa da hare-hare, ta hanyar amfani da dabarun, kunar bakin wake da kwanton Bauna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.