Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnonin arewacin Najeriya sun amince da sake takarar Buhari

Gwamnoni bakwai daga cikin 19 da ke arewacin Najeriya sun nuna goyon bayansu wajen ganin shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sake tsayawa takara zagaye na biyu yayin babban zaben kasar na 2019.

Tun bayan hawansa karagal Mulki a shekarar 2019, Muhammadu Buhari ya yi ta cin karo da kalubalen siyasa daban-daban.
Tun bayan hawansa karagal Mulki a shekarar 2019, Muhammadu Buhari ya yi ta cin karo da kalubalen siyasa daban-daban. Sunday AGHAEZE / NIGERIA STATE HOUSE / AFP
Talla

Gwamnonin bakwai da dukkaninsu an zabe su ne karkashin tutar Jam'iyyar APC mai mulkin kasar, sun ce mafi dacewa shi ne shugaban mai shekaru 75 yanzu haka, ya zarce zuwa zagaye na biyu don ci gaba da gyara kasar.

Dukkanin gwamnonin yayin ganawarsu da shugaban kasar Muhammadu Buhari bayan idar da sallar Juma'a a fadarsa ta Villa da ke babban birnin Najeyar sun nuna goyon bayansu ta da tabbatar da cewa za su yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin shugaban a zarce zuwa zango na biyu.

Gwamnonin da suka hadar da na jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da na Kaduna Nasir El-rufa'i da Yahaya Bello na Kogi sai Simon Lalong na Plateau da kuma Jubrilla Bindow na Adamawa da Ibrahim Geidam Yobe da Abubakar Bello na Niger, sun kuma yi wata ganawar sirri ta musamman da shugaban wadda aka yi ittifakin ta shafi damarar da za su daura don tunkarar zaben na 2019.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.