Isa ga babban shafi
Najeriya

An yi jana'izar fiye da mutane 80 da rikici ya hallaka a Benue

Gwamnatin Benue a tarayyar Najeriya ta yi jana’izar bai daya ga mutane fiye da 80 da aka hallaka Sanadiyyar rikicin makiyaya da Manoma. Kawo yanzu dai babban sufeton ‘yansandan Nijeriya Ibrahim Idris ya isa jihar don tattaunawa kan matakan da za’a dauka da nufin kare afkuwar hakan a gaba.

A cewar hukumomin jihar galibi manoma kan fuskanci makamantan hare-haren daga takwarorinsu makiyaya wanda a lokuta da dama kan haddasa asarar rayuka.
A cewar hukumomin jihar galibi manoma kan fuskanci makamantan hare-haren daga takwarorinsu makiyaya wanda a lokuta da dama kan haddasa asarar rayuka. RFI/Moïse Gomis
Talla

Daruruwan mutane ne suka mutu yayinda dubbai kuma suka gudu don tsira da rayukansu a jihar ta Benue tun bayan barkewar rikici tsakanin Fulani Makiyaya da Manoma daga ranar 31 ga watan Disamba zuwa 9 ga watan Janairu.

Mahukuntan jihar sun ce mutanen sun mutu ne sanadiyyar hare-haren da makiyayan suka kai musu lokacin da suke tsaka da aiki a gonakinsu.

A cewar mataimaki na musamman ga gwamnan jihar ta Benue, Ali Tishahu dukkanin mutanen fiye da 80 da aka yi jana'izarsu manoma ne ciki har da kananan yara da kuma mata galibinsu masu juna biyu.

Bayan kammala Jana'izar babban Sufeton 'yansandan Najeriyar Ibrahim Idris ya jagoranci wata zaman tattaunawa tsakaninsa da mahukuntan jihar kan yadda za a magance makamantan matsalolin a nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.