Isa ga babban shafi
Liberia

Geoge Weah ya gayyaci Arsene Wenger don halartar bikin rantsar da shi.

Kochin kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger ya samu katin gayyata daga tsohon zakaran kwallon kafa kuma shugaban Liberia mai jiran gado Gorge weah don ya halarci bikin rantsar da shi cikin wannan wata.

George Weah ya taka leda a kungiyoin kwallon kafa da suka hadar da Monaco, Paris Saint-Germain, Chelsea da kuma AC Milan.
George Weah ya taka leda a kungiyoin kwallon kafa da suka hadar da Monaco, Paris Saint-Germain, Chelsea da kuma AC Milan. 101 greate goals.com
Talla

A cewar Wenger duk da baya da lokaci amma idan har dakatarwar da hukumar kwallon kafa ke shirin yi masa ta tabbata babu shakka zai halarci taron a Liberia.

Wenger dai ya taba zamowa manajan George Weah a Monaco tsakanin shekarun 1988 zuwa 1992.

Arsene Wenger ya ce yana tuna lokacin da ya hadu da George Weah yana ba kowa ba bai kuma san kowa ba har zuwa lokacin da ya zakara kuma fitaccen dan kwallo a duniya.

A cewar Arsene Wenger za a iya kwatanta tarihin rayuwar George Weah da hikayoyin fina-finai ta yadda yanzu ya kai matsayin da babu wanda ya yi tsammanin hakan a shekarun baya.

Weah, dai ya taka leda a kungiyoyin kwallon kafa da suka hadar da Monaco, Paris Saint-Germain, Chelsea da kuma AC Milan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.