Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya bukaci kawo karshen rikicin Benue

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wata ganawa ta musamman da babban sufeton ‘yansandan kasar Ibrahim Idris dangane da barazar tsaron da ake fuskanta baya-bayan nan a kasar, musamman game da asarar rayukan da ake a jihohin Benue, Rivers da kuma Kaduna.

Muhammadu Buhari ya bukaci babban sufeton ya tabbatar da tsaurara matakan tsaro wajen ganin an kawo karshen asarar rayukan da ake fuskanta.
Muhammadu Buhari ya bukaci babban sufeton ya tabbatar da tsaurara matakan tsaro wajen ganin an kawo karshen asarar rayukan da ake fuskanta. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

A ganawar wadda ta gudana yau a fadar shugaban Najeriyar ta Villa da ke Abuja, Muhammadu Buhari ya bukaci babban sufeton ya tabbatar da tsaurara matakan tsaro wajen ganin an kawo karshen asarar rayukan da ake fuskanta.

Da yake zantawa da manema labarai bayan fitowa daga Fadar shugaban kasar, Ibrahim Idris ya ce rundunar ‘yansandan Najeriyar za ta aike da dakaru na musamman jihar Benue don tabbatar da ganin an magance matsalar tsaron da ake fuskanta.

Sai dai duk da matsalolin kashe-kashen da yanzu haka Najeriyar ke fuskanta, Ibrahim Idris ya ce har yanzu fa akwai ingantaccen tsaro a ilahirin sassan kasar.

Haka zalika babban sufeton Najeriyar ya tabbatarwa al’ummar kasar cewa ba za a kara fuskantar rikice-rikicen da aka samu a baya ba, yana mai cewa jami’ansu na aiki ba dare ba rana wajen ganin an samu dawwamammen tsaro da zaman lafiya a kasar baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.