Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta dau alhakin kai hare-haren karshen shekara

Tsagin kungiyar Boko Haram da ke samun goyon bayan kungiyar IS karkashin Abu Mus’ab Albarnawi ta dauki alhakin kai hare-hare kan barikin soji a karshen shekarar da ta gabata.Sanarwar da IS ta wallafa a shafinta ta ce mayakanta sun kai farmaki barikin soji da ke Kanamma a jihar Yobe tare da hallaka sojoji 9 da kuma kwashe tarin makamai.

Yayin harin na Kanamma mayakan sun hallaka soji tara bayaga jikkata da dama yayinda a bangare guda kuma fiye da 30 suka bace.
Yayin harin na Kanamma mayakan sun hallaka soji tara bayaga jikkata da dama yayinda a bangare guda kuma fiye da 30 suka bace. © AFP PHOTO / BOKO HARAM
Talla

A cewar reshen kungiyar ta IS da ke yammacin Nahiyar Afrika MISWAP ya ce mayakan kungiyar karkashin jagoranci Abu Mus’ab Albarnawi za su ci gaba da kai hare-hare kan dakarun sojin Najeriya.

Kungiyar Boko Haram a karshen shekarar 2017 ta tsannata kai hare-hare dasa bamabamai dama sace mutane yayin bukukuwan karshen shekartar da ta gabata, duk kuwa da kalaman shugaban kasar Muhammadu Buhari na cewa kasar ta shigo sabuwar shekarar a dai dai lokacin da ta yi nasarar fatattakar ayyukan ta’addanci.

Yayin harin na Kanamma mayakan sun hallaka soji tara bayaga jikkata da dama yayinda a bangare guda kuma fiye da 30 suka bace.

Tun a shekarar 2016 ne kungiyar ta rabe gida biyu, inda daya ke karkashin jagorancin Abubakar Shekau daya kuma ke karbar umarni daga Abu Mus’ab Albarnawi wanda ya yi Ikirarin shi da ne ga wanda ya assasa kungiyar Muhammad Yusuf yayinda kuma ya ke samun goyon bayan kungiyar IS.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.