Mali
An naɗa sabon firaministan Mali
Shugaban ƙasar Mali Ibrahim Boubacar Keita ya naɗa tsohon ministan tsaro na kasar Boubeye Maiga domin maye gurbin Abdoulaye Idrissa Maiga a matsayin firaministan ƙasar.
Wallafawa ranar:
Talla
A ranar Juma’a ne tsohon firaministan ya bayar da takardar ajiye mulki tare da sauran jami’an gwamnatinsa, wani mataki da ba a yi tsammani ba.
Hakan na faruwa ne yayin da ya rage watanni kadan kafin gudanar da zaɓen shugaban ƙasar.
Ana sa ran Keita zai sake neman wani wa'adin shugabanci a zaɓen wanda za a yi a shekara mai zuwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu