Isa ga babban shafi
Mali

Firaministan Mali Abdoulaye Idrissa Maiga ya yi murabis

Firaministan kasar Mali Abdoulaye Idrissa Maiga ya gabatarwa Shugaban kasar takardar ajiye aiki a jiya juma’a, bayan share watanni 8 a Gwamnati.

Tsohon Firaministan kasar Mali Abdoulaye Idrissa Maïga
Tsohon Firaministan kasar Mali Abdoulaye Idrissa Maïga HABIBOU KOUYATE / AFP
Talla

Ana ci gaba da cecce kuce bayan murabis na Abdoulaye Ibrahim ,Abdoulaye Maiga wanda ya share watanni takwas a kujerar Firaministan Mali bai bayar da huja zuwa Shugaban kasar kan dalilan da suka kai shi ga yi murabis daga wannan mukamin nasa.

Majiyoyi daga fadar Shugaban kasar ta Mali na bayyana cewa yi haka daga Abdoulaye Idrissa Maiga dake da mukamin mataimakin Shugaban jama’iyya mai mulkin kasar Mali na zuwa ne a dai dai lokacin da ake sa ran Shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita zai sake bayyana takarar sa a zaben Shugabancin kasar na shekara mai zuwa.

Abdoulaye Idrissa Maiga ne Firaminista na hudu a karkashin Shugabancin Ibrahim Boubacar Keita da aka zaba a watan Ogusta na shekara ta 2013.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.