Isa ga babban shafi
Zambia

Cutar kwalara-Gwamnatin Zambia ta nemi agaji daga sojoji

Shugaban ƙasar Zambia Edgar Lungu ya buƙaci sojoji su taimaka wajen kawo ƙarshen yaɗuwar cutar kwalara, wadda ya zuwa yanzu ta hallaka mutane 41 a ƙasar.

Cutar kwalara ta kashe mutane 41 a Zambia.
Cutar kwalara ta kashe mutane 41 a Zambia. AFP PHOTO/Mauricio Ferretti
Talla

A cikin sanarwar da ya fitar, shugaban ya ce ya umurci ɓangarori 3 na dakarun ƙasar su haɗa hannu da ma’aikatar lafiya ta ƙasar domin rage yaɗuwar cutar a babban birnin ƙasar da kuma sauran yankuna.

Tun bayan ɓullar cutar a watan Satumba, a cewar shugaban ƙasar akan samu mutane 60 da ke kamuwa da cutar a kowace rana.

Kwalara cuta ce da ake samun ta daga ruwa mara tsafta, wadda ke da saurin yaɗuwa, kuma an fi alaƙanta ta da yankunan mutane marasa galihu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.