Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 22/07 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 21/07 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 21/07 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 22/07 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 21/07 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 22/07 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 21/07 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 22/07 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 21/07 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 22/07 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 21/07 16h06 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 22/07 16h30 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 21/07 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 21/07 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 22/07 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 21/07 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 22/07 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 21/07 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 22/07 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Afrika

George Weah ya lashe zaben Liberia

media George Weah ya lashe zaben Liberia REUTERS/Thierry Gouegnon

Fitaccen tsohon dan wasan kwallon kafa George Weah ya lashe sakamakon farko na zaben shugabancin Liberia da kashi 61.5 sama da abokin takararsa Joseph Boakai da ya samu 38.5.

Sanarwar da shugaban hukumar zaben kasar Jerome Korkoyan ya bayar bayan kidaya kuri’u sama da kashi 98 cikin 100, ya tabbatar da cewa Weah shi zai maye gurbin uwargida Ellen Johnson Sirleaf da ke kawo karshan wa’adinta a watan gobe.

Tun kafin sanar da wannan sakamako a yau alhamis jami’an ‘yan sanda suka tsaurara matakan tsaro a hedikwatar hukumar zaben kasar, yayin da wasu magoya bayan Weah ke bukukuwan murna.

A wani sakon twitter da ya wallafa a shafinsa, Mista Weah ya ce 'Wannan zabi ne na al'ummar Liberia.'

George Weah ya ce al'ummar Liberia sun yi zabinsu karara

Weah shine ya fi yawan kuri’u a zagayen farko na zaben da aka gudanar cikin watan Oktoba da kashi 38.4 cikin 100, inda ya gaza samun nasaran kashi 50 da ake bukata abinda ya sanya zuwa zagaye na biyu. Boakai shi ne na biyu da yawan kuri’u kasha 28.8 cikin 100.

Tarihin George Weah

George Manneh Weah kamar yadda ake kiransa a Liberia, ya taso ne yankin Clara daya daga cikin kazaman unguwanni masu fama da talauci a birnin Monrovia kuma kakarsa mai suna Emma Klonjlaleh, ita ce ta reni har zuwa lokacin da ya shahara a shekarar 1990 a fannin kwallon kafa.

Tsohon dan wasan wanda ya taba lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya, ya yi kokarin amfani da matsayinsa wajen samun karbuwa a wurin mutanen Liberia.

Shi ne dan wasan Afrika na farko da ya lashe kyautar Ballon d'Or, kuma ya taka leda a manyan kungiyoyin kwallon kafa na Turai da suka hada da PSG da AC Milan da Monaco da Manchester City tsakanin 1989 zuwa 2003, wato lokacin da kasarsa ta Liberia ke fama da yakin basasa.

Siyasa

Weah mai shekaru 51 kuma dan kabilar Kru ya ajiye karatu a lokacin kuruciyarsa amma daga bisani ya samu kwalin digiri bayan ya sha matsin lamba daga ‘yan adawa da ke cewa, ai bai kammala karatu ba, abin da ya sa suke ganin bai shirya zama shugaban kasa ba.

Da dama daga cikin mutanen Liberia musamma matasa na matukar nuna kauna ga Weah saboda rawar da ya taka wajen tallafa musu bayan fama da yakin basasa.

A shekarar 2005 ya fara bayyana sha’awarsa ta tsayawa takarar neman kujerar shugaban kasa, sai dai ya sha kashi a hannun Ellen Johnson Sirleaf, sanna ya sa ke tsayawa a takara a 2011 duk da haka bai kai labara ba.

Weah wanda yanzu Sanata daga yankin Montserado ne ya sake shiga a dama da shi a zaben shugabancin Liberia.

Tsohon dan wasan na da yara uku kuma a can baya ya taba komawa addinin Islama daga Kirista amma daga bisani ya sake sauya sheka.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure