Isa ga babban shafi

Turkiya zata sake ginawa Sudan katafariyar tashar jiragen ruwa

Kasar Turkiya tace zata sake ginawa Sudan tashar jiragen ruwan birnin Ottoman, zalika zata gina sansanin sojin ruwan da zai taimaka wajen samar da tsaro, a wani yunkuri na karfafa alakar soji, da kuma tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan yayin gaisawa da takwaransa na Sudan, bayan sauka a filin jiragen sama na birnin Khartoum.
Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan yayin gaisawa da takwaransa na Sudan, bayan sauka a filin jiragen sama na birnin Khartoum. AP
Talla

Ministan harkokin wajen Sudan Ibrahim Gandour, ya bayyana haka ne bayan ziyarar shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya kai zuwa Khartoum.

Yayin gudanar da ziyarar, shugaba Erdogan ya ce Sudan ta baiwa Turkiya wani sashi na gabar ruwan Suakin, domin gina sansanin yawon bude ido, da kuma hanyar tsallakawa zuwa Makkah ga maniyata aikin Hajji.

Matakin na gwamnatin Turkiya ya zo kasa da watanni uku bayan da kasar, ta bude wani sansanin soji da ta gina a kasar Somalia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.