Isa ga babban shafi
Chadi

Turkiya da Chadi sun sa hannu kan yarjejeniyar bunkasa kasuwanci

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan, ya sanya hannu kan wasu jerin yarjeniyoyi tare da takwaran sa na Chadi Idris Deby, yayin ziyarar da ya kai kasar irin ta na farko da wani shugaban Turkiya ya taba yi.

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan yayin ganawa da shugaban Chadi Idriss Deby, a lokacin da ya kai ziyara birnin N’Djamena.
Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan yayin ganawa da shugaban Chadi Idriss Deby, a lokacin da ya kai ziyara birnin N’Djamena. YASIN BULBUL / AFP
Talla

Erdogan dake dauke da tawagar ministoci da ‘yan kasuwa sama da 100, sun sanya hannu ne kan yarjejeniyar haraji da matasa da wasanni da zuba jari da kuma musayar bayanan asiri.

Shugaban Chadi Idris Deby yace ziyarar zata bude wani sabon babi tsakanin kasashen, yayin da shugabanin biyu suka bayyana matsayin su kan yaki da ta’addanci da kuma matsayin birnin Kudus.

Chad na daga cikin kasashe uku na nahiyar Afrika da Erdogan ya zabi kai wa ziyara.

Ya fara ne da ziyartar kasar Sudan inda ya sa hanu kan yarjejeniyoyin da suka shafi tsaro, sai kuma tattalin arziki kan darajar kudi dala biliyan daya, bayan ganawa da takwaransa Umar al-Bashir.

A halin yanzu shugaban na Turkiya ya isa kasar Tunisia inda zai yi ziyarar karfafa dangantaka ta kwana guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.