Isa ga babban shafi
Masar

Ta'addanci: Kotun Masar ta rataye mutane 15

Mahukuntan kasar Masar sun zartas da hukuncin kisa ta hanyar ratayewa a kan mutane 15, wadanda aka samu da laifin kai wa jami’an tsaron kasar hari.

Wasu jami'an sojin kasar Masar, yayinda suke sintiri a arewacin yankin Sinai. Disamba 1, 2017.
Wasu jami'an sojin kasar Masar, yayinda suke sintiri a arewacin yankin Sinai. Disamba 1, 2017. REUTERS/Mohamed Abd El Ghany
Talla

Da safiyar yau Talata aka zartar da hukuncin kisan a cikin wasu gidajen yari biyu da ke kasar, bayan da wata kotun soji ta same su da laifi.

Kotun da ta yanke hukuncin ta ce mutanen 15, sun kai wa sojojin kasar hari ne a yankin Sinai mai fama da rikici.

Shekaru biyu da suka gabata, wata kotun soji ta zartar da irin wannan hukunci akan mutane 6, da aka samu da laifukan aikata ta’addanci, bayan da suma suka kai hari akan jami’an tsaron kasar.

A makon da ya gabata ne, kungiyar IS ta harba makami mai linzami kan wani filin sauka da tashin jiragen sama a yankin na Sinai, abin da ke nuni da karuwar barazana daga mayakan na IS.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.