Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojin Najeriya sun dakile harin Boko Haram a Maiduguri

A Najeriya wasu da ake kyautata zaton mayakan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari a kauyen Molai da ke wajen birnin Maiduguri na jihar Borno.

Wata majiya ta ce ana jiyo amon musayar wuta tsakanin dakarun sojin da mayakan na Boko Haram.
Wata majiya ta ce ana jiyo amon musayar wuta tsakanin dakarun sojin da mayakan na Boko Haram. REUTERS/Stringer
Talla

Wata majiyar Soji ta ce, an ji karar musayar wuta tsakanin mayakan na Boko Haram da dakarun sojin Najeriyar daga kauyen na Molai mai nisan kilomita biyar daga cikin garin Maiduguri.

Kakakin Sojin da ke Maiduguri ya bayyana cewa sun dakile harin.

A baya-bayan nan dai Mayakan na Boko Haram sun dawo da kai hare-hare sassan kasar musamman yankin arewa maso gabashi inda a nan ne ayyukansu ya fi tsananta, cikin hare-haren kuwa har da wanda suka kai kan jami'an agaji na Majalisar Dinkin Duniya tare da hallaka mutane da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.