Mnangagwa ya zabi Chiwenga a matsayin mataimakinsa
Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya bayyana tsohon babban hafsan sojin kasar da ya jagoranci kawo karshen mulkin Robert Mugabe, Janar Constantino Chiwenga mai ritaya, a matsayin mataimakinsa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Sakataren yada labaran Zimbabawen George Charamba, ya kuma sanar da zabar ministan tsaron kasar Kembo Mohadi a matsayin mataimakin Mnangagwa na biyu.
Sanarwar ta ce aikin dukkanin mataimakan shugaban kasar ya fara aiki ne nan take.
A makon da ya gabata ne Chiwenga yayi ritaya daga mukaminsa na babban hafsan sojin Zimbabwe, wata guda da ‘yan kwanaki, bayan jogarantar sojoji wajen karbe ragamar tafiyar da kasar a ranar 15 ga watan da ya gabata, kafin daga bisani Robert Mugabe ya yi murabus.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu