Majalisar Dinkin Duniya ta fara kwashe bakin-haure daga Libya
Majalisar Dinkin Duniya, ta fara kwashe bakin-haure na nahiyar Afrika daga sansanonin da ake gana musu azaba a kasar Libya zuwa Italiya.
Wallafawa ranar:
Karo na farko kenan da hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar, ta fara aikin kwashe bakin-haure kai tsaye, zuwa nahiyar turai.
Jirgin farko na sojojin Italiya kirar C-130 ya sauka ne a kasar dauke da mata 110, da kuma kananan yara, yayinda jirgi na biyu ke dauke da wasu bakin hauren sama da 50.
Dubban bakin-haure ne ke makale a Libya, inda ake tsare da su, a sansanonin kasar tamkar bayi, tare da gana musu azaba, bayan yunkurin da suka yin a ketarwa zuwa nahiyar turai.
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR ta yi hasashen cewa, akalla bakin-haure dubu 18,000 ake cigaba da tsarewa a sansanoni daban a Libya, kuma nan da shekara mai kamawa, tana sa ran kwashe bakin-hauren akalla 10,000 daga kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu