Rikicin da aka yi ta fama da shi a yankin Pool da ke kudanci, ya shafi aƙalla mutane 130,000 tare da hana gudanar da zaɓen yanki a watan Yuni.
Wakilan gwamnati ƙarƙashin jagorancin Jean Gustave Ntondo da kuma na ɓangaren ƴan tawayen sun sanya hannu kan yarjejeniyar ce a garin Kinkala, da ke a matsayin cibiyar yankin.
Mai Magana da yawun gwamnati Theirry Moungalla ya ce suna maraba da wannan mataki, musamman ma a lokacin da tattalin arzikin ƙasar ya shiga cikin mawuyacin hali.