Isa ga babban shafi
Faransa-Afirka

Taron inganta noma a Faransa

Firaministan Faransa Edouard Philippe ya jagoranci bikin rufe tattaunawa kan yadda za a inganta harkar noma da samar da abinci bayan share tsawon watanni 5 ana tattaunawa.

Edouard Philippe ,Firaministan Faransa
Edouard Philippe ,Firaministan Faransa Reuters/Philippe Wojazer
Talla

Babban kalubalen da mahalarta wannan taro suka share tsawon lokaci suna tattaunawa a kai shi ne yadda za a samar da dokoki domin bai wa manoma kariya, tare da samar da yanayi na kasuwa da kuma farashin irin wanda ya dace da su a wannan zamani.

Christiane Lambert, shugabar babbar kungiyar manoma a Faransa, ta zargi kamfanonin da ke saye tare da sarrafa amfanin gona a matsayin wadanda ke haddasa tarnaki ga manoman kasar, kuma a cewarta ya zama wajibi a cimma matsaya tsakanin bangarorin biyu.

To sai dai Firaminista Edouard Philippe, ya ce nan ba da jimawa ba za a samar da doka da za ta kara daidaita ayyukan masu rabawa da kuma sarrafa amfanin gonar da ake girba a Faransa.

Har ila yau wannan doka ce za ta fayyace irin farashin da ya kamata dillalan amfanin gona su rika samu akan abubuwan da suke saye daga manoman kasar baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.