Isa ga babban shafi
Nijar

Macron ya fara ziyara a Jamhuriyyar Nijar

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya isa Jamhuriyyar Nijar a ziyarar da zai fara yau a kasar wadda ke da nufin karfafa gwiwar dakarun sojin Faransa fiye da dubu 4 da ke aikin yaki da ta'addanci a Nijar.

Ziyarar ta Shugaba Macron na da nufin karfafa gwiwar dakarun da ke yaki da ayyukan ta'addanci a jamhuriyyar Nijar.
Ziyarar ta Shugaba Macron na da nufin karfafa gwiwar dakarun da ke yaki da ayyukan ta'addanci a jamhuriyyar Nijar. REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Bayan saukar shugaban na Faransa Emmanuel Macron ya samu tarbar takwaransa shugaban Nijar Issoufu Muhammadu a filin jiragen sama na Yamai babban birnin kasar inda kuma kai tsaye ya nufi sansanin sojin Faransa da ke cikin filin jirgin saman.

Bayan ziyarar Macron a Gao da Ouagadougou da kuma Abidjan, ziyarar Macron ga Jamhuriyyar Nijar ya nuna yadda shugaban ke da fatan ganin kasashen yammacin Afrikan sun samu ci gaba tare da yakar ayyukan ta’addanci.

Ziyarar ta Macron za ta kaishi har zuwa ranar Kirsimeti inda zai gudanar da bukukuwan Kirsimetin tare da dakarun sojin Faransar da ke yaki da ta’addanci a Kasar.

Kafin wucewar shugaban na Faransa Emmanuel Macron zuwa sansanin sojin sai da su ka yi wata ganawa ta musamman mai tsayi tare da Issoufu Muhammad.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.