Isa ga babban shafi
Uganda

Sojoji sun tarwatsa zaman Majalisa a Uganda

Majalisar Dokokin Uganda yau talata ta dage zaman da ta shirya domin ci-gaba da mahawara kan shirin yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska domin bai wa shugaba Yoweri Museveni damar ci-gaba da zama a kan karagar mulki.

'Yan Majalisar Uganda sun bai wa hammata Iska
'Yan Majalisar Uganda sun bai wa hammata Iska REUTERS/James Akena
Talla

Bayanai sun ce wasu sojoji ne suka kutsa kai Majalisar yau bayan takaddamar da aka samu jiya wadda ta kai ga korar 'yan Majalisu 6 daga zamanta.

Rahotanni sun ce an bai wa hammata iska tsakanin 'yan Majalisan da 'yan Sanda bayan da shugabar Majalisar Rebecca Kadaga ta sanar da dage zaman na yau.

Dokar da ake amfani da ita yanzu ta haramtawa duk wanda ya zarce shekaru 75 takara, wanda ke nuna cewar shugaba Museveni mai shekaru 73 yanzu ba zai iya takara a shekarar 2021 ba, abinda ya sa Majalisar ke nema yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.