An kammala taron ECOWAS karo na 52 a Najeriya
Shugabannin kasashen yammacin Afirka, ECOWAS, sun kammala gudanar da taronsu karo na 52 a Najeriya wanda ya mayar da hankali kan matsalolin da suka shafi tattalin arziki da tsaro da rikicin Siyasa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A lokacin bude taron Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ce kyakkyawar alakar makwabtaka na da muhimmaci ga tsaro da ci-gaban tattalin arziki don haka ya zama wajibi a mayar da hankali wajen yakar barazanar 'yan ta'adda a yammacin afirka.
Kazalika Shugaba Buhari ya tabo batun cinikin Bayi a Libya inda ya ke cewa, 'tallafawa matasa da samar da ayyukanyi zai taimaka wajen dakile kwararar Bakin-haure da ke jefa rayuwarsu cikin hatsari a libya.'
Shugabannin ECOWAS za kuma su yi nazari kan hanyoyin shawo rikicin siyasar Togo da Guinea Bissau, da kuma samar da sauye-sauye kan ayyukan Kungiyar.
Taron dai ya samu halartar shugaban Kungiyar Tarayyar Afirka Moussa Faki da wakilan Majalisar dinkin duniya da kuma tsoffin shugabannin kasashen Afirka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu