Isa ga babban shafi
France-Sahel

Saudiyya da UAE sun ba da tallafin yaƙan ta'addanci a yankin Sahel

Shugaban ƙasar Faransa Emmanuel Macron ya ce ƙasar Saudiya ta yi alƙawarin bai wa rundunar ƙasashe 5 na Sahel da ke yaƙi da ta’addanci a yammacin Afirka kudi Dala miliyan 100. Hadaddiyar Daular Larabawa kuma za ta bayar da Dala miliyan 30.

Taron shugabannin kasashen G5-Sahel da shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Taron shugabannin kasashen G5-Sahel da shugaban Faransa Emmanuel Macron. REUTERS/Ludovic Marin
Talla

Shugaba Macron ya bayar da wannan sanarwa ne a taron da shugabanni Yankin Sahel da Turai suka gudanar a Faransa da nufin ƙarfafa wa rundunar G5-Sahel guiwa.

Ƙasashen na Sahel, wadanda ake wa kallon marasa ƙarfin tattalin arziki su ne Burkina-Faso da Chadi da Mali da Mauritania da kuma Niger.

A lokacin zantawa da manema labaru, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce ya zama wajibi a ci nasara a yaƙin da ake yi da ta’addanci a yankin na Sahel.

00:53

Saurari kalaman Macron a taron G5-Sahel

Haruna Ibrahim Kakangi

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.