A makon daya gabata ne, Majalisar zartaswar Najeriyar ta bukaci kamfanin mai na kasar NNPC ya kawo karshen matsalar karancin man da al'ummar kasar ke fuskanta.
Kawo yanzu dai farashin man a wasu sassan kasar ya kai sama da Naira 180 yayinda kuma duk da hakan ake ci gaba da fuskantar karancinsa a kasar wadda ke takama da arzikin man fetur.
Ko a cikin makon nan Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya ci gaba da fuskantar suka kan yadda ya gaza kawo karshen matsalar man a dai dai lokacin da bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara ke kara kusantowa.
Kusan za a iya cewa karanci da kuma tashin farshin man fetur ya zama ruwan dare a Najeriyar musamman a lokacin shagulgulan al'adu ko na addinai lamarin da wasu ke dora alhakin hakan kan manyan dillan man kasar.