Isa ga babban shafi
Togo

Jam'iyyun adawa sun yi watsi da taron sasantawa da gwamnatin Togo

Kawancen Jam’iyyun adawar kasar Togo da suka kwashe watanni uku suna gudanar da zanga zangar adawa da gwamnatin shugaba Faure Gnassingbe sun bayyana shirin kin halartar taron sasanta rikicin siyasar kasar da gwamnati ta kira.

Kafin yanzu dai dubban magoya bayan jam'iyyun adawar a Togo sun yi ta gudanar da zanga-zanga don nuna adawa da gwamnatin shugaba Faure Gnassingbe tare da fatan kawo karshen shugabancinsa a kasar ta Togo.
Kafin yanzu dai dubban magoya bayan jam'iyyun adawar a Togo sun yi ta gudanar da zanga-zanga don nuna adawa da gwamnatin shugaba Faure Gnassingbe tare da fatan kawo karshen shugabancinsa a kasar ta Togo. REUTERS/Stringer
Talla

Kasashen duniya sun bukaci bangarorin biyu su hau teburin tattaunawa domin kawo karshen rikicin, amma gwamnati ta mikawa Jam’iyyu 5 ne kacal takardar gayyata daga cikin 14, abinda ya sa suka yi watsi da gayyatar.

Mai Magana da yawun Jam’iyyar Brigitte Adjamagbo-Johnson tace sun dauki matsayin kauracewa taron ne saboda yunkurin gwamnati na raba kan su.

A makwannin da suka wuce, shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo da takwaransa na Guinea Alpha Conde sun yi ta kokarin shiga tsakanin domin magance rikicin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.