Faransa
Shugaba Macron ya bayyana Johnny Hallyday a matsayin jarumi
A yau asabar ne Faransawa da hukumomin kasar za su yiwa mawwaki bafaranshe Johnny Halliday ban kwana, bayan isowar gawar sa a wurin nan mai dauke da dimbin tarihi na Champs Elysee dake Paris.
Wallafawa ranar:
Talla
Shugaban kasar ta Faransa Emmanuel Macron ya bayyana marigayin a matsayin jarumi, Macron zai halarci wannan taro, haka zalika tsohon Shugaban kasar Nicolas Sarkozy da ya auratar da Johnny Haliday da Laeticia Hallyday a Neully a shekara ta 1996 ya bayyana cewa zai kasance a wannan wuri.
Johnny Hallyday ya rasu ne daren talata zuwa Laraba ya na mai shekaru 74.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu