Isa ga babban shafi
Kamaru

MDD ta bukaci Kamaru da ta kawo karshen cin zarafi

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci mahukuntan kasar Kamaru da su kawo karshen azabtarwar da jami’an tsaron kasar ke yi wa jama’a a lokacin da suke fada da ayyukan Boko Haram musamman a yankin arewacin kasar.

Wasu daga cikin jami'an tsaron Kamaru
Wasu daga cikin jami'an tsaron Kamaru AFP PHOTO / REINNIER KAZE
Talla

A rahoton da ya fitar, kwamitin yaki da azarbatarwa da kuma cin zarafin bil’adama na Majalisar ya ce, ko shakka babu mayakan Boko Haram sun aikata mummunan ta’adi a yankin arewacin kasar ta Kamaru, to amma kuma akwai hujjojin da ke tabbatar da cewa su ma jami’an tsaron kasar sun ci zarafin jama’a.

Kwamitin ya fitar da wannan rahoto ne ta hanyar tattara bayanai daga shaidu dangane da abubuwan da suka faru tsakanin 2013-2017 musamman a yankin arewacin kasar, in da jami’an rundana ta musamman da ke fada da ayyukan ta’addanci suka kafa cibiyoyi akalla guda 20 da aka tsare jama’a tare da gallaza ma su azaba bisa zargin cewa ‘yan Boko Haram ne ko kuma suna da alaka da su.

Akwai dai bayanai da ke tabbatar da cewa an kashe mutane da dama yayin da wasu suka bata, lamarin da ya sa Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga gwamnatin Kamaru da ta binciki wannan zargi, sannan kuma ta sa ido kan yadda jami’an tsaro ke tafiyar da ayyukansu a yankin.

A cikin watan Yulin da ya gabata, kungiyar Amnesty International ta yi wa jami’an tsaron kasar ta Kamaru irin wannan zargi, duk da cewa kasar na daga cikin kasashen duniya 162 da suka sanya hannu kan yarjejeniyar kasa da kasa da ke hana cin zarafin bil’adama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.