A wata hira da Atiku Abubakar ya yi da wata jaridar kasar da ake wallafawa a karshen mako, ya ce 'ya'yan jam'iyyar da dama sun dawo daga rakiyar shugaban kawai dai sun kasa furtawa ne a fili, inda su ke jiran lokaci nan gaba kadan.
Tsohon mataimakin shugaban kasar, ya ce kowa ya san tafiyarsa, ta yadda ya ke zakulo shahararrun mutane tare da basu dama a fannin da suka kware don ciyar da kasa gaba.
Atiku Abubakar ya ce 'yan Najeriya sun gaji da shugabannin da basa iya yin tunanin yi musu aiki tare da tunanin muhimman batutuwan da za su ciyar da kasa gaba.