Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Congo

Jamhuriyar Congo: An fara sauraron shari'ar 'yan tawaye 36

Kotun sojin jamhuriyar Congo ta fara sauraron karar wasu ‘yan tawayen na kungiyar kasar Kamwina Nsapu su 36, da ake zargi da haddasa hasarar dubban rayuka a rikicin da suka tayar, a babban birnin kasar Kinshasa.

Daruruwan 'yan gudun hijira da rikicin Jamhuriyar Congo ya raba da muhallansu, sun yi jerin gwano domin karbar abinci a sansaninsu na Mpati a yammacin birnin Goma.
Daruruwan 'yan gudun hijira da rikicin Jamhuriyar Congo ya raba da muhallansu, sun yi jerin gwano domin karbar abinci a sansaninsu na Mpati a yammacin birnin Goma. Getty Images/Kuni Takahashi
Talla

Ana zargin ‘yan tawayen 36, da haddasa kazamin rikici a Kinshasa, ciki harda harin da suka kai kan babban gidan yarin kasar, da ya bai wa, fursunoni akalla 4,000 damar tserewa.

Zalika ana zargin mayakan na kungiyar Kamuina Nsapu da kai wasu hare-hare kan ofisoshin ‘yan sanda, wasu cibiyoyin lauyoyi 2 da kuma babbar kasuwar birnin Kinshasa.

Rikicin da ya sake barkewa a sassan kasar ta Jamhuriyar Congo, ya yi sanadiyyar hallaka akalla mutane, 3000.

A makwannin da suka gabata, wata tawagar masu bincike da majalisar dinkin duniya, ta gano wasu manyan kaburbura guda 80 a yankunan da rikicin ya fi kamari.

Zuwa yanzu rikicin ya raba sama da mutane miliyan 1.4 da muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.