Isa ga babban shafi
Zimbabwe

An gurfanar da tsohon ministan kudin Zimbabwe gaban Kotu

An gurfanar da tsohon ministan kudin kasar Zimbabwe, Ignatius Chombo a gaban kotu, bisa zargin cin-hanci da rashawa da kuma yunkurin damfarar babban bankin kasar a shekarar 2004.

Tsohon Ministan kudin kasar Zimbabwe Ignatius Chombo, yayin da jami'an tsaro suka iza keyarsa. ranar 25 ga Nuwamba, 2017.
Tsohon Ministan kudin kasar Zimbabwe Ignatius Chombo, yayin da jami'an tsaro suka iza keyarsa. ranar 25 ga Nuwamba, 2017. REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

Karo na farko kenan da Chombo ya bayyana, tun bayan tsarewar da jami’an soji suka yi masa makwanni biyu da suka gabata kafin murabus din tsohon shugaba Robert Mugabe.

Chombo na daga cikin na hannun daman tsohon shugaba Mugabe, zalika yana daya daga cikin wadanda jam’iyyarsu ta kora a baya-bayan, saboda samunsu da laifin aikata ba dai dai ba.

Al’ummar Zimbabwe musamman masu goyon bayan sabon shugaba Emmerson Mnangagwa, sun bayyana fatan ganin an zartar da hukunci mai tsanani kan Chombo, domin tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.