Isa ga babban shafi
Liberia

Zaben Liberia: Hukumar zabe ta yi watsi da zargin magudi

Hukumar zaben Liberia ta yi watsi da zargin da ake yi mata na yin magudi a zagayen farko na zaben shugaban kasar da aka gudanar.

Dan takarar shugabanci Liberia George Weah
Dan takarar shugabanci Liberia George Weah REUTERS/Thierry Gouegnon
Talla

Kotun Koli ta jinkarta zagaye na biyu na zaben da ya kamata a fafata takanin Joseph Boakai na jam’iyyar mai mulki da George Weah a ranar 7 ga watan Nuwamba kan wannan zargi.

Charles Brumskine na Jam’iyyar Liberty da ya zo na Uku a zaben ne ya shigar da korafin da ya yi sanadi jinkirta zaben.

Sai dai hukumar zaben kasar ta ce jam’iyyu da ke zargin an aikata magudi sun gaza gabatar da hujojjin da ke tabbatar da hakan.

Hukumar ta kuma nuna rashin amincewarta da sake mai-maicin zaben.

Kafin wannan sanarwa, Jam’iyyun da suka shigar da kara sun bukaci jami’an hukumar suyi murabus, tare da cewa zasu daukaka kara a kotun koli.

Yanzu dai kotun kolin kasar ce ta rage ta zartar da na ta hukuncin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.