Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Wanene Mnangagwa?

Sabon shugaban Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa da za’a rantsar a ranar Juma’a, ya ce kasar ta shiga sabon babi na mulkin Dimokuradiyya.

Emmerson Mnangagwa lokaci jawabi gaban al'ummar Zimbabwe a Harare
Emmerson Mnangagwa lokaci jawabi gaban al'ummar Zimbabwe a Harare REUTERS/Mike Hutchings
Talla

Mnangagwa ya bayyana haka ne yayin gabatar da jawabinsa na farko ga al’ummar kasar, bayan komawarsa gida daga kasar Afrika ta Kudu inda ya yi gudun hijira na ‘yan kwanaki.

Batun shawo kan matsalar durkushewar tattalin arzikin kasar da kuma samar da ayyukan yi na daga cikin manyan batutuwan da Emmerson Mnangagwa ya jaddada cewa zai tabbatar, Yayin da ya yi jawabi da dubban al’ummar kasar a hedikwatar jam’iyyar ZANU-PF.

Sai dai wani abu da ya ja hankali shi ne yadda Mnangagwa ya tabbatar da zargin da aka yi a baya na yunkurin hallaka shi.

‘Kwanaki 16 da suka gabata na karbi takardar korata daga mukamin shugaban kasa, bayan awanni biyu da aukuwar hakan na samu bayanan sirri cewar ana shirin hallaka ni, kuma ko a ranar 12 ga watan Agustan da ya gabata an samin guba a abinci domin a wani yunkurin na hallaka ni.'

'Wannan ce ta sa na yanke shawarar maimakon na basu damar ganin bayana, bari na fito na wayar da kan ku al’ummar kasarnan, ku ‘ya’yan jam’iyyar ZANU-PF bisa irin shugabancin kama karayar da ake muku domin in baku damar tabbatar da ra’ayinku’

A ranar Juma’a mai zuwa za’a rantsar da Emmerson Mnangagwa a matsayin Shugaban kasar Zimbabwe, wanda zai karashe wa’adin shugabancin Robert Mugabe mai Murabus, har zuwa ranar 28 ga watan Satumba mai zuwa da za’a sake gudanar da sabon zabe.

Tarihin Emmeron Mnangagwa

An haifi Emmerson Mnangagwa ranar 15 ga watan Satumbar shekarar 1942, kuma ya shiga tawagar masu fafutukar 'yanci a 1960 bayan samun horon soji a kasashen China da Masar, abinda ya sa aka kama shi aka tsare na shekaru 10 a gidan yari.

Bayan samun 'yancin kan Zimbabwe a shekarar 1980, Mnangagwa ya zama ministan tsaro a Gwamnatin Robert Mugabe, inda ya jagoranci murkushe 'yan adawar kasar da kuma kashe dubban mutane.

A shekarar 1983 ya jagoranci kai hari kan 'yan adawa a Yankunan Matabeleland da Midlands, inda daruruwan mutane suka mutu.

A shekara ta 2000 ya zama ministan shari’a har zuwa shekarar 1989 lokacin da ya bayyana shirin kwace gonakin fararen fata, yayin da a shekarar 2008 bayan da shugaba Mugabe ya fadi zabe, Mnangagwa ya jagoranci kai hare-hare kan 'yan adawa har sai da suka janye daga zabe zagaye na biyu.

Shugaba Mugabe ya nada shi mataimakin shugaban kasa ranar 10 ga watan Disamba shekarar 2014, matakin da ake ganin kamar zai bashi damar maye gurbin shugaban, kafin korar sa ranar 6 ga watan Nuwambar bana.

Bayan murabus din Mugabe, jam’iyyar sa ta gayyato Mannagagwa domin maye gurbin sa a matsayin shuagban kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.