Isa ga babban shafi
Faransa-Libya

Faransa ta kira taron gaggawa kan cinikin bayi a Libya

Kasar Faransa ta kira taron kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya domin tattauna matsalar cinikin bayi da ake yi yanzu haka a Libya wanda ake nunawa a hotan bidiyo yanzu haka.

Hotunan cinikin bayi a Libya ya tada hankulan Duniya
Hotunan cinikin bayi a Libya ya tada hankulan Duniya REUTERS/Ahmed Jadallah
Talla

Ministan harkokin wajen kasar, Jean Yves Le Drian ya ce Faransa ta kira wannan taron gaggawa ne saboda girmar matsalar.

Le Drian ya ce hotun bidiyon da ke nuna yadda ake gwanjon mutane a mastayin bayi abin alla-wadai ne da ba za a zura ido ana kallo ba.

Shi ma shugaba kasar Emmauel Macron, ya ce wannan batu bashi da maraba da aikata laifukan yaki, wanda ya zama wajibi a kawo karshan wannan mumunar dabi'a.

Tuni dai wadannan hotunan bidiyo suka tada hankalin jama’a da kuma wasu kasashen duniya, matakin da ya sa wasu suka fara janye jakadun su daga Libya.

Yanzu haka kasar Rwanda ta gabatar da bukatar kwashe 'yan kasashen Afirka da ake cin-zarafin su a Libya domin basu mafaka a cikin kasar ta.

Ministar harkokin wajen kasar Louise Mushikwabo ta ce suna tunanin karbar baki 30,000 daga cikin wadanda yanzu haka suka makale a kasar.

Shugaban kungiyar kasashen Afirka Moussa Faki ya bukaci kasashen Afirka su taimakawa wajen ceto bakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.