Isa ga babban shafi
Kamaru

Kotu za ta fayyace makomar Ahmed Abba 21 ga watan disamba

Sashen daukaka kara na kotun sojin kasar Kamaru, ya tsayar da ranar 21 ga watan disamba mai zuwa domin yanke hukunci dangane da karar da lauyoyin wakilin sashen Hausa na RFI a kasar Ahmed Abba suka shigar, domin soke hukuncin daurin shekaru 10 da aka yanke ma sa.

Ahmed Abba, wakilin RFI Hausa a Moroua
Ahmed Abba, wakilin RFI Hausa a Moroua © RFI
Talla

Bayan sauraren bahashi daga bangaren ma su shigar da kara da kuma na wanda ake tsare da shi, lauyoyin Abba sun bukaci kotun ta sallami wakilin na rfi, saboda ba hujjojin da ke tabbatar da laifin da ake cewa ya aikata, yayin da masu shigar da kara na gwamnati suka bukaci a tabbatar da wannan hukunci.

 

A tsawon sa’o’i uku da aka share ana zaman kotun da ke birnin Yaounde a ranar alhamis, lauyoyin Abba a karkashin jagorancin Maitre Charles Tchoungang, sun sake gabatar da dalilan da ke tabbatar da cewa wanda ake tsare da shi bai aikata wani laifi ba.

 

Ahmed Abba wakilin rfi Hausa a garin Moroua da ke arewacin kasar ta Kamaru, ya share kwanaki 840 tsare a gidan yari, inda ake fatan kotun daukaka karar za ta wanke shi daga laifin yin hulda da ‘yan ta’adda a raanr ta 21 ga watan disamba mai zuwa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.