Jamhuriyar Congo: An fara sauraron shari'ar masu cin zarafin mata
Hukumomin kare hakkin dan adam a Jamhuriyar Demokradiyar Congo, sun sanar da fara sauraron karar mayakan 'yan tawayen da ke gabashin kasar 18, da ake zargi da cin zarafin kananan yara mata 46, ciki har da ‘yar watanni 18 da haihuwa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
An fara shari’ar ce, bayan dagewar da masu fafutukar kare hakkin dan adam suka yi, kan bukatar tilas a hukunta wadanda aka samu da laifi.
A na sa ran shari’ar, zata shafe makwanni ana gudanar da ita.
Kungiyoyin fararen hula na fatan a zartar da hukunci mai tsanani kan jami’an tsaron da ake zargin sun yi amfani da karfi wajen cin zarafin kananan yaran mata a matsayin makamin yaki.
A shekarun 2013 zuwa 2016 ne aka zargi wasu jami’an tsaro da cin zarafin kananan yara a wani kauye mai suna Kavumu a kasar ta Jamhuriyyar Dimukradiyyar Congo.
Masana sun yi hasashen cewa duk da matakan da kasar ke dauka a ‘yan shekarun nan kan jami’an tsaro, dangane da cin zarafi, ko kisan gilla, har yanzu al’amarin na kara kazanta, kasancewa a garuruwan da ke kan iyakar kasar a yankin gabashi, dukkanin bangarorin sojin gwamnati da 'yan tawaye suna yi wa mata fyade a matsayin makamin yaki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu