Zanga-zangar adawa da korar malamai dubu 20 a Kaduna
Gwamnatin jihar Kaduna ta yi Allah wadai da zanga-zangar da kungiyar kwadago ta NLC ta shirya domin adawa da shirinta na korar malaman firamire sama da dubu 20.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A jiya ne shugaban Kungiyar kwadagon Ayuba Waba ya jagoranci wannan zanga-zangar zuwa Majalisar dokokin jihar dan bayyana rashin amincewarsu da matakin korar malaman.
Ita dai gwamnatin jihar Kaduna, ta ce za a sallami malaman daga aiki ne saboda nuna gazawa lokacin da aka gabatar ma su da jarrabawa ‘yan aji hudu domin tantance kwarewarsu, inda sama da dubu 20 daga cikin malamam suka fadi a jarrabawar.
To sai dai shugaban kwadagon sun bayyana jarrabawar a matsayin wadda aka shirya da nufin korar malaman ko ta halin kaka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu