Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Afrika Tsakiya

Kwamitin Sulhu zai tura karin dakaru zuwa Afrika ta Tsakiya

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya yana tattaunawa kan tura karin dakaru 900 zuwa kasar Janhuriyar Afrika ta Tsakiya, domin aikin wanzar da zaman lafiya.

Motocin dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya a kan hanyarsu ta zuwa garin Bambari, na Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.
Motocin dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya a kan hanyarsu ta zuwa garin Bambari, na Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya. © RFI/Pierre Pinto
Talla

Matakin ya biyo bayan gargadin da Antonio Guterres, Sakatare Janar ko Magatakardan Majalisar Dinkin Duniyar yayi na cewa rikicin kabilanci da zai kai ga yunkurin shafe wata kabila na iya barkewa a kasar.

Zalika karkashin daftarin da kasar Faransa ta mikawa kwamitin tsaron ke nazari a kai, za’a tsawaita wa’adin aikin rundunar wanzar da zaman lafiya ta majalisar MINUSCA a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya har zuwa watan Nuwamba na shekarar 2018.

Faransa ta kuma bukaci da a tura karin jami’ai masu sa’ido kan ayyukan rundunar ta MINUSCA 480, wadanda zasu aiki tare da jami’an ‘yan sanda dubu 2, 080 sai kuma sojoji da yawansu zai karu zuwa dubu 11, 650 idan aka amince da tura Karin dakarun 900.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.