Isa ga babban shafi
Sudan

Sansanonin ‘yan gudun hijira sun koma tamkar kasuwanni – Al Bashir

Shugaban Sudan Umar Hassan Albashir, ya ce lokaci ya yi na rufe illahirin sansanonin ‘yan gudun hijira da ke kunshe da milyoyin mutane a yankin Darfur wanda ya share tsawon shekaru yana fama da yakin basasa.

Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir.
Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir. REUTERS/Mohamed Nureldin Abdallah
Talla

Albashir ya ce an kawo karshen matsalolin da yankin ya yi ta fama da su, dan haka mataki na gaba shi ne rufe sansanonin domin kowa ya koma gidansa.

Shugaban ya yi zargin cewa sansanonin ‘yan gudun hijira a yankin na Darfur sun zama tamkar wani dandali ko kasuwa ga kungiyoyin bada agaji, inda suke daukar hotunan ‘yan gudun hijira su mikawa gwamnatocin kasashe domin a basu kudaden da zasu taikamaka musu, daga bisani kuma su karkatar da kudaden.

A farkon wanna shekara, kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya rage yawan dakarun wanzar da zaman lafiya da ya tura zuwa yankin na Darfur mai fama da rikici a baya, lamarin da ya dada tabbatar da fara samun kwanciyar hankali a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.