Isa ga babban shafi
Congo Dimokuradiyya

Hukumar zaben DRC ta fitar da ranakun zaben kasar

Hukumar zaben Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, ta bayyana ranar 23 ga watan disambar 2018 a matsayin ranar zaben shugabancin kasar, na ‘yan majalisar dokoki da kuma na larduna.

Joseph Kabila Shugaban Jamhuriyar Demokradiyyar Congo cikin nazarin yiyuwar zabe a kasar
Joseph Kabila Shugaban Jamhuriyar Demokradiyyar Congo cikin nazarin yiyuwar zabe a kasar Dr Meddy
Talla

A karkashin yarjejeniyar da aka kulla tsakanin ‘yan adawa da shugaban kasar Joseph Kabila, ya kamata a gudanar da zaben ne kafin karshen wannan shekara, abin da ya sa ko ‘yan adawar suka bayyana rashin amincewa da wannan sabon jadawali da hukumar zaben ta fitar yayin da bangaren gwamnati ke marhabin da shi.

Ga baki daya kungiyoyin farraren hula da jam’iyyu adawa sun bukaci yan kasar da su fito domin nuna adawar su dangane da wannan shiri daga hukumar zaben kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.