Isa ga babban shafi
Liberia

An dage zaben Shugabancin kasar Liberia

Kotun Kolin kasar Liberia ta umurci Hukumar zabe ta gudanar da bincike kan zargin da yan adawa suka yi na tafka magudi a zaben da ya gudana.

Kotun kolin kasar Liberia
Kotun kolin kasar Liberia REUTERS/James Giahyue
Talla

Shugaban alkalan kotun Francis Korkpor yace an haramtawa Hukumar zaben gudanar da zaben zagaye na biyu da aka shirya yi gobe talata, har sai ta gudanar da bincike kan korafin da Jam’iyyar Liberty ta gabatar.

Kotun ta gargadi Hukumar zabe da ta kaucewa sanya wata ranar gudanar da zaben na gaba ba tare da an kamala binciken ba.

George Weah da mataimakin shugaban kasa Joseph Boakai ke takara zagaye na biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.