Isa ga babban shafi
Sierra-leone

"Dala miliyan 6 da aka ware don yakar cutar Ebola sun yi batan dabo"

Kungiyar bada agaji ta kasa da kasa Red Cross ta ce akalla dala miliyan 6 da aka ware domin yaki da cutar Ebola a yammacin Afrika sun yi batan dabo.

Wani jami'in lafiya mai kula da masu cutar Ebola a kasar Guinea
Wani jami'in lafiya mai kula da masu cutar Ebola a kasar Guinea KENZO TRIBOUILLARD / AFP
Talla

Kungiyar ta Red Cross ta ce tana zargin an hada baki ne da ma’aikatan bankin da aka dana kudaden da kuma wasu ma’aikatanta wajen yashe miliyoyin dalolin.

A halin yanzu kungiyar ta ce tana aiki da hukumar yaki da cin hanci da Rashawa ta kasar Saliyo don bankado dukkanin wadanda ke hannu cikin badakalar.

Sama da mutane dubu 11,000 ne suka mutu a dalilin annobar cutar ta Ebola da ba’a taba ganin barkewarta ba a tsakanin 2014-2016.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.