Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 22/01 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/01 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/01 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 22/01 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/01 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 22/01 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/01 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 22/01 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 21/01 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/01 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/01 16h06 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 21/01 16h30 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/01 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/01 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 21/01 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/01 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 21/01 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/01 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 21/01 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Afrika

'Yan kasar Senegal sun lashe tallafin samun horon aikin Jarida

media Marie-Christine Saragosse shugabar kafafen yada labaran Faransa, da Cécile Mégie babbar Darakatar rfi, tare da 'yan kasar Senegal da aka karrama da basu kyautar tallafin bada horo a aikin jarida, yayin bikin da ya gudana ba daba tallafin a Senegal © Abdoulaye Diaw

An sanar da sunayen wadanda suka lashe tukuicin samun horo a karkashin gasar da aka yi wa taken ‘’Ghislaine Dupont da kuma Claude Verlon’’, ma’aikatan Radio France International da ‘yan ta’adda suka kashe a Mali shekaru 4 da suka gabata.

An bayar da tukuicin ne ga wani dan jarida mai suna Arouna Diof da kuma wani Injiniyan daukar sauti mai suna Nicole Diedhiou, lokacin wani biki da aka gudanar a birnin Dakar na kasar Senegal.

Shugabar kafafen yada labaran Faransa da ke yada shirye-shirye zuwa kasashen ketare Marie-Christine Saragosse, ta ce matakin bada tukuicin shi ne nunawa ‘yan ta’adda cewa har abada ba zasu iya sanya yawa ‘yan jarida gwiwa ba.

Wannan ne karo na hudu da za a bayar da wannan dama ga dan jarida daya da kuma jami’in daukar sautin rediyo daga kasashen Afrika renon Faransa, a bikin da ya samu halartar Marie-Christine Saragosse shugabar kafafen yada labaran Faransa da ke watsa shirye-shirye zuwa ketare, da Cécile Mégie babbar Darakatar rfi, da kuma ‘yan uwa da dangin Ghislaine Dupont da Claude Verlon.

A Karon farko dai an sanar da sakamakon gasar ne a kasar Mali, sai na biyu a Madagascar yayin da a bara aka sanar da sakamakon a Jamhuriyar Benin.

Ana dai gudanar bikin ne a ranar da aka kebe domin kawo karshen cin zarafin ‘yan jarida a duniya.

A shekara ta 2014 ne aka kashe ma’aikatan na Radio France International a kusa da garin Kidal na arewacin Mali, a daidai lokacin da suke gudanar aikinsu.

A daidai lokacin da aka cika shekaru hudu da faruwar wannan lamari ne aka samu bayanan da ke tabbatar da cewa biyu daga cikin mutane ukun da ake zargi da aikata kisan na zaune ne a cikin kasar Algeria.

'Yan kasar Senegal sun lashe tallafin samun horon aikin Jarida 03/11/2017 - Daga Nura Ado Suleiman Saurare

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure